Romans 14

1Ku karbi duk wanda yake da rarraunar bangaskiya, ba tare da sukar ra’ayinsa ba. 2Wani yana da bangaskiyar yaci komai, wani wanda yake da rauni yakanci ganye ne kawai.

3Kada wanda yake cin komai ya raina wanda baya cin kowanne abu. Kada kuma wanda baya cin kowanne abu ya shara’anta sauran da suke cin komai. Saboda Allah ya karbe shi. 4Kai wanene, kai wanene da kake ganin laifin bawan wani? Tsayawarsa ko faduwarsa ai hakin maigidansa ne, amma Ubangiji yana da ikon tsai da shi.

5Wani yakan daukaka wata rana fiye da sauran. Wani kuma yana daukan ranakun daidai. Kowa ya zauna a cikin hakakkewa akan ra’ayinsa. 6Shi wanda ya kula da wata rana, ya kula da ita don Ubangiji. Kuma wanda yaci, yaci ne domin Ubangiji, domin yana yi wa Allah godiya. Shi wanda bai ci ba, yaki ci ne domin Ubangiji. Shima yana yi wa Allah godiya.

7Domin babu wanda yake rayuwa don kansa a cikinmu, kuma babu mai mutuwa don kansa. 8Domin in muna raye, muna raye don Ubangiji. Kuma in mun mutu, mun mutu ne don Ubangiji. Ashe, ko muna raye, ko a mace mu na Ubangiji ne. 9Domin wannan dalilin Almasihu ya mutu ya kuma tashi, saboda ya zama Ubangiji ga matattu da rayayyu.

10Amma ku don me kuke shara’anta yan’uwanku? kai kuma don me kake raina dan’uwanka? Dukan mu zamu tsaya gaban kursiyin shari’ar Allah. 11Domin a rubuce yake, “Na rantse, “inji Ubangiji”, kowacce gwiwa zata rusuna mani, kowanne harshe kuwa zai yabi Allah.”

12Domin kowannenmu zai fadi abin da shi yayi da bakinsa a gaban Allah. 13Saboda da haka kada muyi wa juna shari’a, amma maimakon haka ku dauki wannan kudduri, don kada kowa ya zama sanadin tuntunbe ko faduwa ga dan’uwansa.

14Na sani na kuma tabbata tsakani na da Ubangiji Yesu, ba abin da yake mara tsarki ga asalinsa. Sai dai ga wanda ya dauke shi marar tsarki ne yake zama marar tsarki. 15Idan har abincinka na cutar da dan’uwanka, ba ka tafiya cikin kauna. Kada ka lalata wanda Yesu ya mutu domin sa da abincinka.

16Saboda haka, kada abubuwan da aka dauka kyawawa su zama abin zargi ga wadansu. 17Saboda mulkin Allah ba maganar ci da sha ba ne, amma game da adalci ne, salama, da farin ciki a cikin Ruhu Mai Tsarki.

18Domin wanda yake bautar Almasihu a wannan hanya, karbabbe ne ga Allah, kuma jama’a sun yarda da shi. 19Don haka, mu nemi abubuwa na salama da abubuwan da zasu gina juna.

20Kada ku lalata aikin Allah don abinci. Komai yana da tsarki, amma kaiton mutumin da yake cin abin da zai sa shi ya fadi. 21Bashi da kyau a ci nama ko a sha ruwan inabi, ko duk abin da zai jawo faduwar dan’uwanka.

22Wannan bangaskiyar da kuke da ita, ku adana ta tsakaninku da Allah. Mai albarka ne wanda zuciyarsa bata da laifi akan abin da hankalinsa ya ga daidai ne. Duk wanda yayi shakka amma kuma yaci, ya sani yayi laifi kenan, domin ba tare da bangaskiya bane. Duk abin da ba na bangaskya bane zunubi ne.

23

Copyright information for HauULB